16 Mayu 2026 - 22:31
Source: ABNA24
Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Da Dama A Najeriya

Kafofin yada labarai sun ba da rahoton cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari tare da sace ɗalibai da dama a jihar Borno da ke Najeriya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr, mazauna jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya sun shaida wa kamfanon dillancin labarai na Reuters da AFP cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace ɗalibai da dama.

Wani mazauni mai suna Ubaidullah Hassan, wanda yake zaune kusa da makarantar, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ‘yan bindigar sun kai hari a makarantar Firamare da Junior Secondary School ta Musa da ke unguwar Askira-Uba da misalin karfe tara na safe (8:00 agogon GMT) a daidai lokacin da ake gudanar da darussa, inda suka tafi da dalibai da dama.

Wani malamin makarantar ya shaida wa Reuters cewa maharan dauke da bindigogi sun zo ne a kan babura.

Malamin ya ce: "Duk da cewa wasu daga cikin daliban sun gudu zuwa cikin daji, zan iya gaya muku cewa an sace da yawa daga cikinsu."

Har ya zuwa yanzu, babu wani mutum ko kungiya da ta dauki alhakin wannan harin da ke da alaka da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha